BUGUN ZUCIYAR MASOYA 001
«FURTA SO GA MASOYA»
Samun Sukuni da Sauqin Gudanar da Alamura Cikin Nishadi, Maza Sunyi Guluwwi (Wuce Gona da Iri) Mata Sunyi Ilhadi (Sakaci) Awannan ´Bangaren Anaida Soyayya Yazama dodo ko Baqar damisa muna Sakaci da ita Ayayinda Tazama Ginshiqi Agaremu Kuma Hutuce ga Zuqatanmu,<br />
Tabbas Soyayya tana Wanzar da Farin ciki Azuciyar Maiyinta da Sauqi Sannan Takan Zamo Cuta ga Zuciyar Wanda Yake Sakaci da ita Kuma Yayi wasa da Alamarinta.
Wasu Sun mutune Saboda Boye Soyayya Aransu Bisa Rashin Bayyanar da Hakkin Zuciyarsu Har Dama Yawuce musu Sannan Wasu kuwa Sunyi Aure da Soyayyar Wani Zaman Aure Yaqi Yimasu Dadi Saboda Wanda Suka So abaya.
Soyayya Makamice Muyi Qoqarin Adanata Ama'aji Mai inganci Sannan Kada Mu Cutar da kanmu Kokuwa mucutadda Wasu Domin Sun Mallaka mana Zuciyoyinsu, Akwai wani Yanayi Da Mutum Ke Shiga In Yana Soyayya, Baya Sha'awar Magana Duk da Zuciyarsa Cike Take Da Bayanai, Zai Ke Jin Kadaici Amma Yayinda Baison Kowa Ya Kulashi.
Zai Rika Jin Kwadayin Hawaye Amma(Hawayen) Bazai Fita Ba, Qila Sai Yayinda Ya Samu Wanda Zai Bawa Labarin Zuciyarsa!
Ance, Ba Gurinda Yafi Duniyar Soyayya Dadi, Sai Kaje Kaji Tafi Duk Kurkuku Qunci Da Azaba, Babu Yanayi Mafi Quna Kamar Na Wanda Ga Harshensa Nanan Kuma Ba Kurma bane Amma Hawayensa Ke Maka Magana kuma Bakaji!
Sau dayawa Hakan Na Faruwane Saboda Wasu Yanayin A Soyayya, Hakika Masu Soyayya Abun Tausayawa Ne, Ku Daure Ku Bada Lokacinku Dan Jin Labarin Zuciyar Dake Cikin Kunci Saboda Ku, Ku Faranta Ransu Da Kalmomi Masu Dadi, Hakika Kuma Ubangiji Zai Faranta Ranku Ko Ba A Wannan Lokaci Ba.
ﻣﻦ ﻧﻔﺲ ﻋﻦ ﺃﺧﻴﻪ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻛﺮﺑﺔ ﻣﻦ ﻛﺮﺏ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻧﻔﺴﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺑﺔ ﻣﻦ ﻛﺮﺏ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ
"Duk Wanda Yayewa Dan Uwansa Wani Qunci Ciki Kuncin Duniya, Shima Allah Zai Yaye Masa Qunci A Ranar Alqiyama.
Allah Karabamu da Danasanin Duniya da Qiyama.
Post no: 001
Created at 2022-04-26 23:58:07
Back to posts
UNDER MAINTENANCE