SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP
YIN AIKI DOMIN ALLAH {5}
Yaku musulmai! Kamar yadda muka yi bayani a baya cewa, ikhlasi yakan cutu da wasu abubuwa, kamar jiji-da-kai, da neman sakamako na duniya akai aikin ibada. To duk wani abu da zai zama cikas ga ikhlasi to shari’a ta tanadin maganinsa.
Maganin jiji-da-kai shi ne mutum ya riqa ganin baiwar da Allah ya yi masa da falalar da yayi gare shi. Kuma duk wani abu da zai aikat to daga falalar Allah ne. Allah yana cewa:
(وَلَوْلَا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ مَا زَكَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ أَبَدًا) [النور: ٢١].
(Ba domin falalar Allah gare ku ba da rahamarsa, to da babu wani daga cikinku da zai tsarkaka har abada. Sai dai Allah shi ne yake tsarkake wanda ya so).
Hakanan maganin neman abin duniya akan aikin da’a, wanda yin haka yana cutar da ikhlasi, shi ne, bawa ya san fa cewa shi tsantsar bawa ne ga Allah. Don haka don ya yi wa Ubangijinsa hidima ba zai ce, haqqi ne akan Ubangijinsa sai lalle ya biya shi. Duk abin da Ubangiji zai ba shi na sakamako falala ce ta Allah gare shi.
Kamar yadda yana daga cikin abubuwa da suke cutar da ikhlasin bawa, idan yayi wani aiki ya riqa jin ya gama gamsuwa da aikin da ya yi. Magnanin irin wannan lamari abu biyu ne:
Na farko: Ya riqa hango gajiyawarsa, da kasawarsa, ya kuma gane cewa akwai nasibin shaidan da son zuciya a tattare da shi. Duk qarancin aiki da wuya ne ka samu shaidan ba shi da wani nasibi a cikinsa. An tambayi Manzon Allah game da waiwaye a sallah, sai ya ce, «Wani abu ne da shaidan yake sata daga sallar bawa». Ka ga fa wannan waiwaye ni kadan yayi da idonsa, amma ga abin da ya kasance. To ina ga wanda zuciyarsa ce zai ta waiwayi wanin Allah?!
Hanyar magani ta biyu: Ita ce, bawa ya san cewa Allah yana da haqqoqi diyawa akansa saboda kasancewar bawan Allah ne. Kuma bawa bai isa ya ce, zai biya Allah duk haqqoqinsa da suke kansa. To don me ba zai ji kunyar zuwa ga Allah da dan aikinsa ba. Don haka wajibi ne ya riqa tuhumar kansa akai-akai. Duk bawan da ba ya tuhumar kansa akai-akai to wannan jahili ne, mai rudar kansa.
الله تعالى أعلم
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Telegram
https://t.me/joinchat/SoaVkBryqONVNGyU8dDpLQ
DAKA SHEIK ALBANY DA'AWA GROUP GA MASU SAN SHIGA GROUP KO AIKO DA TAMBAYA ZASU IYA TUROWA TA WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA 08179713163
[3/19, 3:10 AM] +234 817 971 3163: SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP
YIN AIKI DOMIN ALLAH {6}
Yaku bayin Allah! Akwai wasu abubuwa da zasu taimaka bawa wajen ikhlasinsa bayan taimakon Allah. Wadannan abubuwa kuwa su ne:
Bawa ya sa Allah a zuciyarsa koda yaushe. Yayi aikinsa domin Allah. Ya riqa neman agajinsa yana cewa: *«Ya Hayyu Ya qayyum, bi rahmatika Astagith”.
Abu na biyu mutum ya san cewa, mutane ba sa amfanarwa kuma ba sa cutarwa. Don haka mu ma daina kawo su a tunaninmu yayin da muka wata ibada.
Bawa ya guji zuciyarsa mai umartar sa da mummunan aiki. Wacce take neman girma da fariya, da girma da yabo, da wulaqanta mutane, da nuna musu girman kai, da yi musu izgili.
Mu guji shaidan la’ananne. Ka mu sake ya biyo mana ta inda ba ma tsammani. Kamar wajen hira, ko alfahari, ko nuna kishi ga addini. Ko lokacin da mutane za su riqa yabonsa suna nu sha’awarsu da abin da yake yi.
Yaku bayin Allah!
Ku riqa halarto da Allah yayin ayyukanku. Ku sanya sirrinku ya zama mafi tsarkaka daga zahirinku. Ku sani Allah ya san asiran bayinsa, babu wani abu da yake buye masa a sama ko a qasa. Mu Karanta fadar Allah da yake cewa:
(وَمَا تَكُونُ فِي شَأْنٍ وَمَا تَتْلُو مِنْهُ مِنْ قُرْآَنٍ وَلَا تَعْمَلُونَ مِنْ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُودًا إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ وَمَا يَعْزُبُ عَنْ رَبِّكَ مِنْ مِثْقَالِ ذَرَّةٍ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَلَا أَصْغَرَ مِنْ ذَلِكَ وَلَا أَكْبَرَ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُبِينٍ) [يونس: 61]
(Babu wani sha’ani da za ka kasance a cikinsa. Kuma babu wani abu da kake karantawa na al’qur’ani, ko wani aiki da kuke yi face mun zamo muna halarce lokacin da kuke aikata shi. Kuma babu wani da yake buya ga Ubangijinka a qasa yake ko a sama, ko mafi qanqanta daga haka, ko mafi girma face yana cikin littafi mabayyani).

DAKA SHEIK ALBANY DA'AWA GROUP GA MASU SAN SHIGA GROUP KO AIKO DA TAMBAYA ZASU IYA TUROWA TA WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA 08179713163[3/19, 3:05 AM] +234 817 971 3163: SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP